Lafiya Jari Ce
Haɗarin cizon mahaukacin kare da ke haddasa cutar zangai maras jin magani
- Author: Vários
- Narrator: Vários
- Publisher: Podcast
- Duration: 0:09:28
- More information
Informações:
Synopsis
A wannan makon shirin na lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan matsalar cutar zangai ko cizon mahaukacin kare, cutar dake daɗa bazuwa a jamhuriyyar Nijar musaman a Jihar Maradi, jihar dake sahun gaba wajan masu fama da wannan matsala. Alƙaluman ofishin ministan lafiya na jamhuriyyar Nijar sun nuna cewa cikin mutane 10 da cutar ta kashe, 5 sun fito ne daga jihar Maraɗi, inda aka ga sabbin kamuwa da wannan cuta a tare da mutane har 95. Babban ƙalubalen wannan cuta shi ne rashin maganin iya samun waraka matuƙar aka kamu, ta yadda masu lalurar zasu riƙa haushi da cizo da kuma tirje-tirje irin na kare, yayinda sukan iya yaɗa cutar ga duk wanda suka ciza. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.