Lafiya Jari Ce

Illolin da ke tattare da sauya launin fata da wasu mata ke yi

Informações:

Synopsis

Shirin lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda mata suka rungumi tsarin gyaran jiki ta fannoni daban-daban kama daga magungunan sha ko mayukan shafawa ko kuma salon amfani da na’ura da nufin ƙawata sura. Wasu daga cikin batutuwa mafi jan hankali a wannan babi na gyaran jiki shi ne tayar da komaɗar fata da sauran sassan jiki don killacewa ko kuma kange kai daga bayyanar tsufa, kuma guda cikin tsarin da ake amfani da shi shi ne na’urorin zamani wanda ƙwararru a wannan fanni na fata gashi da kuma ƙumba ke cewa kafin yanzu abin bai samu karɓuwa a Najeriya ba.