Bakonmu A Yau

Aminu Bala Sokoto kan alwashin sabon ministan tsaron Najeriya

Informações:

Synopsis

Sabon ministan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa mai ritaya ya sha alwashin murƙushe barazanar ƴan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin jama’ar Najeriya, inda ya ce nan gaba kaɗan jama’a za su ga gagarumin sauyi. Janar Musa wanda ya yi rantsuwar kama aiki a cikin makon nan, ya sanar da wasu daga cikin tsare-tsaren da zai yi amfani da su a sabon salon yaƙi da ta’addancin da zai faro, ciki har da mayar da ilahirin sojoji bakin daga don fatattakar ɓatagari da kuma hana biyan ƴan ta’addan fansa dama kawo ƙarshen sulhu dasu. Dangane da wannan ne Azima Bashir Aminu ta tattaunawa da masanin tsaro Squadron Leader Aminu Bala Sokoto. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.