Bakonmu A Yau

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 1:33:54
  • More information

Informações:

Synopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodes

  • Tattaunawa da Dr Kabiru Adamu kan tashe tashen hankula a lokutan zaɓe

    Tattaunawa da Dr Kabiru Adamu kan tashe tashen hankula a lokutan zaɓe

    12/11/2026 Duration: 03min

    Ƙwamitin zaman lafiya na Janar Abdussalmi Abubakar ya ce a cikin makwanni 10 da suka gabata, an samu tashe tashen hankiula da ke da nasaba da zaɓe 109 wajen gangamin siyasa, wanda ya haɗa da kai hare hare a kan magoya bayan wata jami'iyya. Ƙwamitin ya ce matsalar ta fi ƙamari a jihohin Kaduna da Enugu da EDo da kuma Enugu abin da ke jefa fargaba a tsakanin jama;a. Shiga lamar sauti don sauraron cikakkiyar hira da Dr Kabiru Adamu na Beacon Security, mai nazari a kan tahe tashen hankula.....

  • Nijar ta gayyaci wakilin EU a ƙasar kan zargin yi mata katsa landan

    Nijar ta gayyaci wakilin EU a ƙasar kan zargin yi mata katsa landan

    11/11/2026 Duration: 03min

    An shiga takun-saƙa tsakanin gwamnatin mulkin sojin Nijar da ƙungiyar Tarayya Turai EU a gefe guda  da kuma Aljeriya a ɗaya gefen tun bayan wasu kalamai da babban jami’in diflomasiyyar  ƙungiyar ya yi a kwanan baya inda ya bukaci Aljeriya ta fito ta yi mata  karin haske dangane da dalilin jibge wani bangare na dakarunta a arewacin Jamhuriyar Nijar. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar da Intchinikar Alhasan masanin tsaro a jamhuriyar Nijar......

  • Tattaunawa da Zainab Muhammad kan nasarar Flamingos ta lashe kofin duniya

    Tattaunawa da Zainab Muhammad kan nasarar Flamingos ta lashe kofin duniya

    10/11/2026 Duration: 03min

    A Najeriya ana ci gaba da yabawa tawagar ƴan wasan Flamingos ta mata ƴan ƙasa da shekaru 17 da suka kafa tarihin zama tawaga ta farko da ta lashe kofin duniya karon farko a tarihin Nahiyar Afrika. Wannan na nufin babu wata ƙasa a Afrika da ta taɓa lashe wannan kofi, in banda Najeriya a wannan karo. Zainab Muhammad guda ce daga cikin masu bibiyar harkokin wasanni a duniya, yayin tattaunawarta da Rukayya Abba Kabara ta ce ba shakka waɗannan ƴan mata sun yi wasa da jajircewa, ga dai yadda zantawar tasu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawarsu..

  • Alhaji Sa’adu Gulma shugaban ƴan Arewa mazauna Kudancin Najeriya ƴan jam’iyyar APC

    Alhaji Sa’adu Gulma shugaban ƴan Arewa mazauna Kudancin Najeriya ƴan jam’iyyar APC

    09/11/2026 Duration: 03min

    Yayin da ƴan siyasa suka fantsama gadan-gadan domin yaƙin neman zaɓe a Najeriya, kusan dukannin jam’iyyu na ci gaba da zawarcin ƴan asalin Arewacin ƙasar da ke zaune a yankin Kudanci saboda muhimmacin ƙuri’unsu. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Sa’adu Yusuf Ɗandare Gulma, shugaban ƴan Arewa mazauna jihohin Kudancin Najeriya mabiya jam’iyyar APC mai mulki, domin jin irin rawar da suke takawa a wannan tafiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu...............

  • Isa Sanusi kan yadda Amnesty ke tir da kaiwa ƴan adawa hare-hare a Najeriya

    Isa Sanusi kan yadda Amnesty ke tir da kaiwa ƴan adawa hare-hare a Najeriya

    06/11/2026 Duration: 03min

    Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana matuƙar damuwa game da hare haren da ake kai wa ƴan adawa a Najeriya, musamman ganin abinda ya faru a jihar Kebbi wajen taron jam'iyyar ADC. Rahotanni sun ce an raunata wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar tare da lalata motocin su. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Malam Isa Sanusi, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai.

  • Farfesa Adam Muhd Abubakar taron shekara-shekara na kasuwar hannayen jari a Najeriya

    Farfesa Adam Muhd Abubakar taron shekara-shekara na kasuwar hannayen jari a Najeriya

    05/11/2026 Duration: 03min

    Yau ake ƙarƙare taron masu ruwa da tsaki kan hada-hadar kasuwar hannayen jari a Najeriya, wanda ya saba gudana a duk shekara. Taron na bana da ke gudana a birnin Lagos, ya mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da bunƙasa gami da ƙarfin jarin kasuwar ta hada-hadar hannayen jari, wajen samar da ayyukan yi, da bunƙasa masana’antu da kuma taimaka wa marasa ƙarfi. Kan wannan Ahmed Abba, ya tattauna da Farfesa Adam Muhd Abubakar, ƙwararre a fannin harkokin banki da hada-hadar kuɗi a bisa tsarin Musulunci. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

  • Tattauna wa da Jawad Ango kan yadda zaɓen tsakiyar waadi ya gudana a Amurka

    Tattauna wa da Jawad Ango kan yadda zaɓen tsakiyar wa'adi ya gudana a Amurka

    04/11/2026 Duration: 03min

    Jam’iyyar Democrat ta samu rinjaye a dukkanin majalisun wakilai da Dattijan Amurka yayin zaɓen tsakiyar wa’adin da ƙasar ta gudanar a jiya Talata, inda sakamako ke nuna cewa ta samu kujeru 186 a majalisar wakilai yayinda Republican ta samu kujeru 114 ake kuma dakon sakamakon yankuna 7, can a majalisar dattawar kuma Democrat ɗin ta samu kujeru 52 Republican 40 wanda kuma dama bisa ƙa’ida kujeru 51 ake buƙata gabanin samun rinjaye a wani yanayi da ake dakon sakamakon yanki guda wato kujera 1 da walau ta zama ta ɓangaren adawar ko kuma ta jam’iyya mai mulki. Wannan mataki kai tsaye na nuna cewa shugaba Donald Trump ya rasa rinjaye a dukkanin zaurukan majalisun ƙasar, kodayake an jiyo shi yana amsa shan kaye tare da fatan aiki tare da ƴan Democrat. Khamis Saleh ya zanta da Jawad Madugu Ango, mazaunin ƙasar ta Amurka dangane da yadda zaɓen ya gudana dama ƙalubalen da ke gaban shugaba Trump a shekaru biyun da suka rage masa. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............

  • Shuaibu Sharafaddeen akan zaɓen tsakiyar waadi na Amurka

    Shu'aibu Sharafaddeen akan zaɓen tsakiyar wa'adi na Amurka

    03/11/2026 Duration: 03min

    A wannan Talatar Amurkawa ke kaɗa kuri’a a zaɓen Tsakiyar Wa’adi wanda sakamakonsa ka iya sauya alƙibilar jagorancin majalisar dattawa da ta wakilai da a yanzu haka ke samun rinjayen jam’iyyar Republican ta shugaba Donald Trump. Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Alh. Shu’aibu Sharafaddeen wanda ya shafe kimanin shekaru 20 yana zaune a Amurka, inda yake cewa, zaɓen na tattare da alheri.

  • Hamisu Shira akan fitar da jerin sunayen waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuria

    Hamisu Shira akan fitar da jerin sunayen waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a

    02/11/2026 Duration: 02min

    Shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya Farfesa Joash Amupitan, ya ce sai a ranar 15 ga watan Dsiamba mai zuwa ne hukumar za ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka cancanci kaɗa kuri’unsu a zaɓukan da za a yi cikin shekara mai zuwa. Farfesa Amupitan wanda ke ganawa da manyan kwamishinonin hukumar ta INEC a birnin Port Hacourt da ke jihaer Rivers, ya tabbatar da cewa za a gudanar da dukannin zaɓukan a ranakun da aka tsara ba tare da wani sauyi ba. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Hon Hamisu Mu’azu Shira, tsohon shugaban kwamitin zaɓe a Majaisar Wakilan Najeriya, domin jin yadda yake kallon kamun lodoyin hukumar tra INEC a wannan karo.

  • INEC ta maido da sunayen wasu daga cikin ƴan takarar da ta cire daga zaɓen 2027

    INEC ta maido da sunayen wasu daga cikin ƴan takarar da ta cire daga zaɓen 2027

    30/10/2026 Duration: 03min

    Hukumar zaɓen Najeriya ta mayar da sunayen wasu ƴan takarar gwamna da kujerun majalisu da ta cire daga zaɓen 2027. Matakin ya biyo bayan nazari a kan ƙorafe ƙorafen da INEC ɗin ta karɓa daga hannun jam'iyyun siyasa, yayin da taƙi amincewa da wasu. Daga cikin waɗanɗa aka sanya sunayen su har da ɗan takaran gwamnan Kano Abdusalam Gwarzo da na Gombe Isa Ali Pantami. Kan wannan lamari Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Abdulmajid Lawan Waziri. 

  • Dr Umar Kwairanga kan kammala sayar da hannayen jarin matatar Dangote

    Dr Umar Kwairanga kan kammala sayar da hannayen jarin matatar Dangote

    29/10/2026 Duration: 03min

    Katafaren kamfanin Aliko Dangote ya sanar da cewar masu zuba jari daga ƙasashe 120 ne suka sayi hannayen jarin matatar sa da ke Lagos, wadda ta samu riɓi uku na kuɗaɗen da ta shirya samu a kasuwar hannayen jarin. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce wasu majiyoyi na daban guda biyu da ke da masaniya kan cinikin hannayen jarin, sun ce matatar ta samu kuɗin da ta sarai za ta samu har sau uku, kuma naira triliyan 6 da biliyan ɗari 4 ko kuma dala biliyan 4 da miliyan ɗari 7 da 80 daga cikin Najeriya suka fito. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da DR Umar Kwairanga, shugaban hukumar hada hadar hannayen jarin Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai

  • Tattaunawa da Barr Abdullahi Jalo kan gano musabbabin mutuwar masu haƙar maadinai a Neja

    Tattaunawa da Barr Abdullahi Jalo kan gano musabbabin mutuwar masu haƙar ma'adinai a Neja

    28/10/2026 Duration: 03min

    Kwamitin binciken da gwamnatin Najeriya ta kafa domin gano dalilan da suka yi sanadiyyar mutuwar mahaƙan zinare 33 a komar hukumar tsaron Civil defence a birnin Minna na jihar Neja ya bayyana cewa rashin iska ne ya sanya matasan sumar da ya kai ga rasa rayukansu yayinda wasu 44 kuma galabaita kodayake an yi nasarar ceto rayuwarsu. Kwamitin ya buƙaci biyan diyya kan dukkanin mamatan 33 baya ga 44 da suka tsira da rayukansu yayinda kuma ya bayar da shawarar gaggauta korar kwamandan rundunar ta Civil Defence a jihar Neja dama ialhirin jami'an da suka kai ga wannan sakaci. Barr Abdullahi Jalo na ɗaya daga cikin dattawan da suka buƙaci gudanar da binciken gaggawa lokacin afkuwar lamarin kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi bayan fitar wannan sakamakon bincike. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu....

  • Aminu Halilu kan kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2026 da Kane ya lashe

    Aminu Halilu kan kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2026 da Kane ya lashe

    27/10/2026 Duration: 03min

    Kyaftin ɗin tawagar kwallon ƙafar Ingila Harry Kane ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa ta Ballon d’Or, inda ya zama ɗan wasan ƙasar na farko cikin shekaru 25 da ya lashe wannan kyauta, bayan da ya doke Kylian Mbappe and Lamine Yamal. Wannan ne dai karo na farko da aka gudanar ba bikin bada kyautar a wata ƙasa saɓanin Faransa, tun bayan da aka farota shekaru 70 da suka gabata. Kan haka Khamis Saleh ya tattauna da Aminu Halilu Tudun Wada, mai sharhi kan lamuran wasanni don jin yadda suka kalli kyautar ta bana. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............

  • Ibrahim Salissou kan tura sojojin Aljeriya zuwa Nijar da za a yi

    Ibrahim Salissou kan tura sojojin Aljeriya zuwa Nijar da za a yi

    26/10/2026 Duration: 03min

    Majalisun dokokin Aljeriya, sun bai wa gwamnati damar tura sojojin ƙasar zuwa  Jamhuriyar Nijar, kwanaki uku bayan da ministocin ƙasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu. Aljeriya da Nijar ƙasashe ne da suka raba iyakar mai tsawon sama da kilomita 900, yayin da ake kallon yankin iyakar a matsayin wanda fatake ke amfani da shi domin gudanar da safara iri-iri. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da mai magana da yawun ƙawancen wasu ƙungiyoyin da ke fafutukar ƴantar da nahiyar Afirka FRSA, Ibrahim Salissou, domin jin yadda suke kallon wannan batu na bai wa Aljeriya damar jibge sojoji a Nijar. Ku latsa alamar sauto domin jin yadda tattaunawarsu ta kasance...........

  • Farfesa Tukur AbdulƘadir kan fargabar rikici gabanin zaɓen Najeriya a 2027

    Farfesa Tukur AbdulƘadir kan fargabar rikici gabanin zaɓen Najeriya a 2027

    23/10/2026 Duration: 07min

    Yayin da Jam'iyyun siyasa suka ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensu a sassan ƙasar gabanin zaɓen shekara mai zuwa, rahotanni na bayyana fargabar da ake da ita na samun tashe tashen hankula tsakanin magoya bayan jam'iyyun daban daban. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da farfesa Tukur Abdulkadir na Jami'ar Jihar Kaduna a kan wannan fargaba da kuma illar da ka iya yi wa shirin zaɓen. Sai a latsa alamar sautin da ke sama domin sauraron tattaunawar....

  • Prof Balarabe Sani Garko kan mai ɗauke da cutar Ebola da aka samu a Najeriya

    Prof Balarabe Sani Garko kan mai ɗauke da cutar Ebola da aka samu a Najeriya

    22/10/2026 Duration: 03min

    Mazauna birnin Abuja da ke Najeriya sun shiga ruɗani sakamakon samun mai ɗauke da cutar Ebola da akeyi, wadda ta kai ga samun aƙalla mutane 44 da suka yi mu'amala da ita. Hukumomin ƙasar ta bakin ministan lafiya Farfesa Ali Pate sun bayyana ɗaukar matakan da suka dace domin ganin cutar bata bazu ba. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko, na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu................

  • Tattaunawa da Pharmacist Ayuba Tanko kan hukunta masu samar da magungunan jabu

    Tattaunawa da Pharmacist Ayuba Tanko kan hukunta masu samar da magungunan jabu

    21/10/2026 Duration: 03min

    Ƙungiyar Jami'an kula da magunguna da PSN a Najeriya ta buƙaci gwamnatin ƙasar da ta tsaurara dokar hukunta kamfanoni da ɗaiɗaikun mutanen da ke sarrafa magunguna na bogi waɗanda ke sanadiyyar salwantar rayukan jama'a Shugaban ƙungiyar na ƙasa Pharmacist Ayuba Tanko Ibrahim ya ce suna buƙatar sanya tarar miliyan 5 tare da ɗaurin rsakanin shekaru 5 zuwa 20 a kan duk wanda aka samu samu da aikata irin waɗannan laifuka, saɓanin tarar naira dubu  biyar zuwa goma da ake karɓa a hannun masu laifin yanzu bisa tanadin dokokin Najeriya. Kan hakan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƙungiyar na ƙasa Pharmacist Ayuba Tanko Ibrahim. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawarsu.

  • Dr Ladan Salihu kan tsaikon fidda ɗan takara ɗaya na adawa da zai kara da Tinubu

    Dr Ladan Salihu kan tsaikon fidda ɗan takara ɗaya na adawa da zai kara da Tinubu

    20/10/2026 Duration: 03min

    Yayin da lokacin gudanar da zaɓen shekara mai zuwa a Najeriya ke ci gaba da ƙaratowa, ga alama yunƙurin ƴan adawa na gabatar da ɗan takara guda domin tinkarar shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na daɗa dakushewa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Ladan Salihu, jigo a jam'iyyar ADC. Ku latsa alamar sauti domin jin yadda zantawar ta su ta kasance..............

  • Auwal Jibril kan shirin farfaɗo da kasuwanci tsaƙanin Najeriya da Faransa

    Auwal Jibril kan shirin farfaɗo da kasuwanci tsaƙanin Najeriya da Faransa

    19/10/2026 Duration: 03min

    Yanzu haka wata tawagar Najeriya da ta ƙunshi jami’an gwamnati da kuma ƴan kasuwa, tana gudanar da ziyara a Faransa inda ta tattauna da mahukuntan ƙasar kan yadda za a haɓaka kasuwanci a tsakanin ƙasashen biyu. Batun bayar da dama ga ƴan Najeriya domin shigar da kayan amfanin gona a Faransa, shi ne abu mafi muhimmanci da aka share kusan makon ɗaya ana tattaunawa a kai, kamar dai yadda ɗaya daga cikin ƴan kasuwar na Najeriya Alhaji Auwal Jibril, shugaban kamfanin Azuretti Services and Distribution da ke dillancin kayan amfanin gona daga Najeriya ya kasance a cikin  tawagar, ga kuma ƙarin bayanin da ya yi wa Abdoulkarim Ibrahimn Shikal.

  • Za mu ƙona motoci 250 muddin ba a bamu makamanmu ba – Ƴan ta’adda

    Za mu ƙona motoci 250 muddin ba a bamu makamanmu ba – Ƴan ta’adda

    16/10/2026 Duration: 08min

    Wasu Ƴan ta'adda a Jihar Zamfara da ke Najeriya sun yi barazanar ƙona motoci 250 sakamakon harin da aka kai musu a Ƴankin Ɗansadau, inda aka kashe wasu daga cikinsu tare da ƙwace bindigoginsu da kuma babura. Sanarwar da ƴan ta'addan suka yi, na zuwa ne bayan fara ƙona motocin da suka yi, inda suka ce dole sai an dawo musu da bindigogi da kuma babur ɗin da aka kwace, yayin da suka fara kai hari wasu ƙauyuka. Kan wannan lamari Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ɗaya daga cikin Dattawan Najeriya da suka fito daga yankin, Sanata Sa’idu Ɗansadau. Sai a latsa alamar sauti da ke sama domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.....

page 1 from 2