Synopsis
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episodes
-
Yadda ƙabilar Tangale dake Bombe a Najeriya suka gudanar da bikin shekara-shekara
29/07/2025 Duration: 10minShirin na wannan mako ya mayar da hankali ne aka wata al'adar al'umar Tangale dake jihar Gomben Najeriya wacce a shekara ke haɗo kan ɗaukacin al'uma na ciki da wajen ƙasar. A alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.
-
Yadda al'adar bikin cika ciki ta jima tana cin kasuwa a ƙasar Hausa
22/07/2025 Duration: 10minShirin na wannan mako ya yi duba ne kan al'adar nan da ta jima tana cin kasuwa a ƙasar Hausa, wato Sallar cika ciki da ake gudanarwa bayan Sallar layya. Tsawon shekaru da wannan al’adar ta dore,ake kuma ci gaba da gudanar da ita a wurare da dama. Al'ummar Hausa da dama a birane da karkara a duk ranakun tara da goma ga watan farko na shekarar musulunci wato Muharram, sukan gudanar da azumin da kuma raya al'adar nan mai suna cika ciki wato dai sai kaci ka koshi kuma abinci mai dadi, wasu kan amfani da iya abinda suke da shi, yayinda wasu suke karawa da hidindimu. Wani abin lura shine, yadda a yankunan karkara, idan wannan lokaci ya ƙarato, jama’a musaman mata na dukufa ne ɓangaren girki, inda a wajen gida yara matasa kan ɗora sanwa wasu lokutan su kan yi amfani da haka wajen raya al’adar nan da aka sani da aci a cika ciki sannnan ga nishaɗi. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Tasirin al'adar ''Mai suna'' ko Takwara ga ƙabilar Kanuri a Jamhuriyyar Nijar
15/07/2025 Duration: 10minShirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan guda cikin al'adun Ƙabilar Kanuri can a kudu maso gabashin Jamhuriyyar Nijar, Al'adar da ake yiwa laƙabi da ''Mai suna'', al'adar da ke da matuƙar tasiri a cikin wannan ƙabila da ke da matuƙar yawa a ƙasashen Najeriya da Nijar da kuma Kamaru. Al'adar ta Mai suna ko kuma takwara, na cikin al'adu masu matuƙar girma a wannan ƙabila da kuma ke da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ƴan uwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Tasirin rubuce-rubuce wajen alkinta al'adun gargajiya
01/07/2025 Duration: 10minShirin al'adun mu na gado na wannan rana ya mayar da hankali kan gudunmowar marubuta wajen adana gargaji da tsrain al'adu Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa