Wasanni

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:58:42
  • More information

Informações:

Synopsis

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Episodes

  • Tasirin wasannin sada zumunta ga manyan ƴan wasa a lokacin hutun manyan Lig

    07/07/2025 Duration: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya mayar da hankali kan wasanni da ke gudana a lokacin hutu, ta yadda manyan ƴan wasa daga lig lig na Turai da sauran nahiyoyi ke komawa gida don doka wasannin sada zumunta a irin wannan lokaci, lamarin da ke nishaɗantarwa da kuma ƙara danƙon alaƙa tsakanin manyan ƴan wasan da masu tasowa. A cikin shirin zakuji tattaunawa da masana a fannin na wasanni da kuma tsaffin ƴan wasa game da muhimmancin irin waɗannan wasanni na sada zumunta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Kwara da Rivers sun lashe kofin ƙalubale na Najeriya a bangaren Mata da Maza

    30/06/2025 Duration: 09min

    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya mayar da hankali ne kan wasannin ƙarshe na gasar cin kofin ƙalubale na Najeriya, wadda yanzu ake kira President Federation Cup, da aka gudanar a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena da ke birnin Lagos.  Da wasan mata aka fara, inda aka ɓarje gumi tsakanin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Nasarawa Amazons da ke garin Lafia da Rivers Angels ta birnin Fatakwal a wansan ƙarshe karo na 10 a wannan gasa, ɓangaren mata. Ƴan matan Nasarawa ne suka fara saka ƙwallaye biyu a ragar Rivers, ƙwallayen da Rukayyat Shola Sobowole ta ci, a yayin da Taiwo Ajibade da Taiwo Afolabi suka farke wa Rivers. Haka dai aka tashi wannan wasa biyu da biyu, Rivers mairiƙe da kofin ta sake daukawa a wannan karon a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ci 4 da 2. Bayan wasan na mata, da baye-bayen kyautuka ne aka shiga wasan maza, inda kungiyar ƙwallon ƙafa ta Kwara United ta garin Ilorin ta doke Abakaliki FC da ci 4 da 3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da aka buga can

  • Shirye-shiryen sun yi nisa na fara gasar Firimiyar Najeriya ta baɗi

    23/06/2025 Duration: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni a wanan mako ya yi dubu ne kan shirye-shiryen fara gasar Firimiyar Najeriya ta kaka mai zuwa, kuma tuni hukumar shirya gasar Firimiyar Najeriya wato NPFL, ta sanya 22 ga watan Agusta mai zuwa a matsayin ranar soma kaka ta baɗi. An dai ji shugaban hukumar shirya babbar gasar ta Najeriya Gbenga Elegbeleye na cewar, suna duba yuwuwar soma amfani da na’urar VAR a gasar mai zuwa, baya ga kuma inganta kayayyakin gudanarwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............

  • An bude gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi a Amurka

    16/06/2025 Duration: 09min

    Shirin Duniyar wasanni na wanan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne akan gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi da aka bude a karshen mako a ƙasar Amurka dama sauye -sauyen da aka samu a bana.  Ku shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shiri........

page 2 from 2