Synopsis
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episodes
-
Illar ta'ammali da magungunan ƙara kuzari ko rage gajiya da jama'a ke yi
22/12/2025 Duration: 09minShirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan karon ya mayar da hankali kan yadda ɗabi’ar ta’ammali da wasu nau’ikan tsumin gargajiya da sunan samun kuzari ko kuma ƙarfin jiki ke ci gaba da ta'azzara tsakanin jama'a, wanda masana suka yi ittifaƙin na da matuƙar illa ga lafiyar jama’a. Tsumi na baya-bayan nan da ke samun karɓuwa tsakanin jama’a musamman masu ayyukan ƙarfi shi ne ‘’Wankin ciki’’ ko kuma Gyaran Gida ko kuma Aji Garau kamar yadda wasu ke kiranshi, tsumin da ke ɗauke da magungunan gargajiya, kuma ya ke ci gaba da samun karɓuwa tsakanin dukkanin rukunin mutane kama daga matasa da kuma magidanta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Dabarun yaƙi da ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma Obesity tsakanin matasa
15/12/2025 Duration: 09minShirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir a wannan mako ya mayar da hankali kan wasu alƙaluman mujallar Lancet da ke nuna cewa nan da shekarar 2050 fiye da kashi 50 na yawan al’ummar Afrika musamman Afrika za su zama masu ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma Obesity a turance. Alƙaluman na Lancet wanda aka tattara bayan gwaji a ƙasashe fiye da 50 ya nuna cewa matsloli masu alaƙa da cimaka da kuma rashin motsa jiki su ke matsayin kan gaba da za su haddasa wannan matsala ta Obesity ko kuma ƙibar da ta wuce ƙima. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Bincike ya gano cewa kashi 38 na matan Damagaram ne kaɗai ke haihuwa a asibiti
08/12/2025 Duration: 10minShirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali game da yadda wasu mata a Jamhuriyyar Nijar ke ƙin amincewa da haihuwa a asibiti duk kuwa da haɗarin da ke tattare da haihuwa a gida. Wasu alƙaluman baya-bayan nan da mahukuntan jihar Damagaram suka tattara, ya nuna cewa ƙasa da kashi 40 na mata ne ke haihuwa a asibiti duk kuwa da yadda mahukunta suka mayar da haihuwar kyauta a asibitocin jihar waɗanda aka samar da su a gab da jama'a. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Kamaru ta yi nasarar rage mutuwar mata yayin haihuwa a cikin shekaru 4
01/12/2025 Duration: 10minA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan wasu alƙaluma da ke nuna cewa cikin shekaru 4 da suka gabata Kamaru ta yi nasarar rage yawan matan da ke mutuwa a lokacin haihuwa ko kuma goyon ciki. Alƙaluman hukumar kula da lafiyar yara da na DHS mai tattara alƙaluman jama’a sun nuna da cewa da kusan rabi ne aka samu raguwar mace-macen matan, inda daga mace-macen mata dubu 2 cikin dubu 100 a 2018 adadin a yanzu ya dawo mace-macen mata 406 cikin dubu 100 duk shekara wanda ke nufin gagarumar nasara, kodayake ministan lafiya na ƙasar Manaouda Malachie ya ce sun yi amfani da wasu tsare-tsare gabanin samun wannan nasara.