Bakonmu A Yau

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 1:25:11
  • More information

Informações:

Synopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodes

  • Ba mu taɓa bai wa wani ɗan ta’adda ko anini ba – Malam Uba Sani

    12/11/2025 Duration: 03min

    Dai dai lokacin da wasu jita-jita ke nuna cewa mahukuntan Najeriya kan biya kuɗaɗen fansa ga ƴan bindiga gabanin kuɓutar da ɗimbin mutanen da suke garkuwa dasu, ko kuma ga waɗanda suka aje makamansu a jihohin arewa maso yammacin ƙasar, Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi iƙirarin cewa bai taɓa biyan ko sisin kwabo ga ƴan bindiga ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Gwamna Uba Sani da Khamis Saleh................

  • Abubakar Ibrahim kan taron sauyin yanayi na COP30 da ke gudana a Brazil

    11/11/2025 Duration: 03min

    An bude traon Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi da ake kira COP 30 a Brazil inda masana muhalli da sauyin yanayi daga kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare muhallin ke halarta a kasar Brazil. Za'a kwashe makwanni biyu ana gudanar da wannan taro wanda zai mayar da hankali a kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a kan wannan matsala. Dakta Abubakar Ibrahim, Malami kuma mai bincike a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ya yi tsokaci a kan matsalar musamman ganin irin illar da take yi a yankin arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawarsa da Bashir Ibrahim Idris.

  • Gwamnatin Yobe za ta gina sabon asibitin ƙoda a Gashua inda cutar tafi ƙamari

    10/11/2025 Duration: 03min

    Gwamnatin Jihar Yobe dake Najeriya tace za ta ƙara gina manya asibitoci a kananan Hukumomi 3 wadda suka hada da Gashua, Potiskum da kuma Nguru, baya ga gina wani wannan sabon asibitin kula da masu fama da cutar ƙoda a Garin Gashua inda cutar tafi ƙamari a jihar. Haka kuma gwamnatin ta ce zata gina wasu makarantu na musamman a kowacce mazaɓa 178 da ake da su a jihar domin ƙara inganta karatun tun daga tushe. Gwamna Jihar, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da wakilinmu  Bilyaminu Yusuf. Latsa alamar sauti don jin tattaunawarsu....

  • Barr Abdullahi Jalo kan ƙoƙarin warware barazanar Trump na kai hari Najeriya

    06/11/2025 Duration: 03min

    Yayin da ake ci gaba da lalubo hanyar warware matsalar barazanar Donald Trump na kai hari Najeriya, wasu masana na bayyana cewar ta hanyar diflomasiya kawai za a iya warware wannan dambarwa. Barr Abdullahi Ibrahim Jalo na ɗaya daga cikin su. Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris ta gudana..............

page 2 from 2