Bakonmu A Yau

Informações:

Synopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodes

  • Engr Yabagi Sani kan yadda 'yan adawa ke kallon dambarwar mafi karancin albashi

    05/06/2024 Duration: 03min

    Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun sanar da dakatar da yajin aikin da suka fara ranar litinin saboda kasa kulla yarjejeniyar albashi mafi karanci da ya dace a biya ma'aikata. A yanzu dai gwamnatin ta ce a shirye take ta biya albashin da ya zarce naira dubu 60, yayin da ake ci gaba da tattaunawa a tsakanin bangarorin biyu. Ko yaya 'yan adawa ke kallon wannan dambarwa, tambayar kenan da Bashir Ibrahim Idris ya yiwa Injiniya Yabagi Sani, tsohon 'dan takaran shugaban kasar Najeriya. Ku latsa alamar sauti don jin yadda tattaunawarsu ta gudana.......

  • Farfesa Usman Muhammad kan nakasu da jam'iyar ANC ta samu a zaben Afrika ta Kudu

    04/06/2024 Duration: 03min

    A karon farko a cikin shekaru 30 da suka gabata, Jam'iyyar ANC mai mulkin kasar Afirka ta kudu ta gaza samun galabar da za ta kafa gwamnati ba tare da kawance ba a zaben da aka yi a kasar, abinda ke nuna yadda jama'a suka fara juya mata baya. Ganin irin tagomashin da jam'iyyar ta samu karkashin shugabanninta na farko irin su Nelson Mandela da Thabo Mbeki, ko me ya sa ta gamu da wannan koma baya?  Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Usman Muhammad na Cibiyar horar da 'yan majalisu dake Abuja.Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar zantawar ta su.......

  • Alhaji Hima Barkire kan matakin hana motocin dakon kayan Benin shiga cikin Nijar

    03/06/2024 Duration: 03min

    Mahukunta a Nijar sun ce ba za su bari motocin da ke ɗauke da lambar Jamhuriyar Benin damar tsallaka iyakar ƙasar da Najeriya domin shiga ko kuma fita daga Nijar ba, a maimakon haka, sai dai su zagaya zuwa cikin Burkina Faso da kuma Togo kafin komawa gida. Wannan dai alama ce da ke ƙara tabbatar da cewa alaƙa ta yi tsami a tsakanin ƙasashen biyu tun daga lokacin da aka kifar da gwamnati Mohamed Bazoum. Dan gane da wannan mataki, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Hima Barkire, sakataren tsare-tsare na ƙungiyar masu motocin dakon kaya a Nijar.Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawar ta su......

  • Abdulaziz Abdulaziz kan cikar Tinubu shekara guda a karagar mulkin Najeriya

    30/05/2024 Duration: 03min

    A jiya ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara guda a karagar mulki, kuma RFI Hausa ta samu tattaunawa da mai bashi shawara akan harkokin yada labarai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, a kan batutuwa da dama da suka kunshi tattalin arziki, noma, tsaro, darajar naira da kuma kuncin rayuwa. Ga kadan daga cikin tattaunawar da suka yi da Bashir Ibrahim Idris.

  • Sanata Mamman Abubakar Danmusa kan cika shekaru 25 da dimokiradiyar Najeriya ta yi

    29/05/2024 Duration: 03min

    Yau Najeriya ke cika shekaru 25 da dawowar tafiyar wannan mulkin dimokiradiyar, wadda ke bai wa jama'a damar zabin shugabanin da suke so su jagorance su. Wannan dai za a iya cewa karo na farko da mulkin farar hular ya mike ba tare da katsewa ba. Dangane da wannan ci gaba, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawan kasar a Jamhuriya ta 2, Sanata Mamman Abubakar Danmusa. Ku danna alamar sauti don jin zantawar su ta gudana........

  • Hajiya Naja'atu Muhammad kan takaddamar masarautar Kano

    27/05/2024 Duration: 03min

    Yayin da ake ci gaba da dakon kawo karshen rikicin sarautar Kano da ke Najeriya a gaban kotu, masu fada aji daga ciki da wajen Kano, ciki harda majalisar sarakunan Arewacin Najeriya da kungiyar dattawan yankin sun bukaci taka tsan tsan da kuma kwantar da hankalin jama'a tare da kai zuciya nesa domin kaucewa tashin hankali. A bangare guda kuma an fara samun masu zanga zanga, yayin da hukumomin tsaro ke gargadin jama'a da su kaucewa karya doka. Dangane da wannan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Naja'atu Muhammad, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.Ku tsala alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawar tasu.....

  • Farfesa Abba Gambo kan gargaɗin manoma a game da shuƙin wuri a damunar bana

    22/05/2024 Duration: 03min

    Rahoton wanda National Bureau of Statistic ta fitar a makon da ya gabata, ya cewa an fuskacin hauhawan farashin kayayyaki da sama da kashi 33 da rabi cikin 100 a watan Afrilun da ya gabata.

  • Prof. Tukur Abdulkadir kan zargin Firaministan Isra'ila da aikata laifukan yaki

    21/05/2024 Duration: 03min

    Kotun Duniya ICC ta zargi Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaron sa tare da shugabannin Hamas da aikata laifuffukan yaki.Wannan mataki ya haifar da cece kuce sakamakon irin asarar rayuka da ake ci gaba da yi a Gaza da Gabar yamma da kogin Jordan da kuma Rafah. Dangane da tasirin matsayin kotun da kuma abinda zai yi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir na Jami'ar Jihar Kaduna.Ku latsa alamar sauti domin jin yadda zantawar su ta gudana...

  • Hon Sama'ila Muhammad a kan dokar kare hakkin Yara a Najeriya

    20/05/2024 Duration: 03min

    'Yan Najeriya na ci gaba da tafka mahawara a kan dakatar da auran wasu marayu 100 da ministar kula da harkokin matan kasar ta bukata a Jihar Neja, saboda abinda ta kira sabawa dokar kare hakkokin yara.Yanzu haka kungiyoyi daban daban sun ruga kotu domin kalubalantar ministar.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da lauya kuma tsohon 'dan majalisar tarayya, Hon Samaila Muhammed, wanda yace dokar da ake magana a kai ta sabawa dokokin kasa.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren hirar.

  • Farfesa Abba Gambo kan matakan da gwamnatoci ke dauka a Najeriya game da noma

    16/05/2024 Duration: 03min

    Yanzu haka damina ta fara sauka a wasu sassan arewacin Najeriya, yayin da manoma ke shirin tinkarar aikin gona gadan gadan domin magance matsalar karancin abincin da kuma tsadar shi da aka fuskanta. Dangane da shirye shiryen noman, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abba Gambo, mai bai wa gwamnonin Najeriya shawara a kan aikin noma. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu..........

  • Attahiru Bafarawa kan shirin ƴan adawa na tinkarar jam'iyya mai mulki a 2027

    15/05/2024 Duration: 03min

    A Najeriya, yanzu haka wasu daga cikin manyan ‘yan adawar ƙasar cikin su harda wadanda suka tsaya takarar zaɓen shekarar 2023 sun fara tintibar juna domin tsara yadda za su tinkari jam’iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa. Rahotanni sun ce akwai yiwuwar kafa wata sabuwar jam’iyya domin kalubalantar gwamnati mai ci.Dangane da wannan yunkuri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa. Kuna iya latsa alamar sauto domin sauraren hirar.

  • Farfesa Kailani Muhammed a kan batun satar danyen mai a Najeriya

    14/05/2024 Duration: 03min

    Hukumomin Najeriya sun ce sun kama jiragen ruwa 14 da ake satar danyan man fetur a Neja Delta tsakanin watan Janairun wannan shekara zuwa karshen watan Maris.Rundunar dake aikin samar da tsaro a Jihar Rivers tace wannan bai hada da kananan jirage 90 da kuma mutane 74 da ta kama ba, wadanda ke yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Kelaini Muhammed, masani a kan harkar gas da man fetur, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

  • Kwamandan MNJTF Janar Ibrahim Sallau kan nasarar su a yankin tafkin Chadi

    09/05/2024 Duration: 06min

    Rundunar hadin gwuiwa da ke yaƙi da mayakan Boko Haram a Tafkin Chadi da ake kira MNJTF ta sanar da kashe mayaka 299 a cikin watanni 10 da suka gabata da kuma samun wasu 273 da suka mika kansu cikin lumana. Kwamandan rundunar Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali ya bayyana haka ga Babban Editan sashin Hausa Bashir Ibrahim Idris a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho bayan ya kwashe watanni 10 yana jagorancin rundunar mai cibiya a kasar Chadi.Ku latsa alamar sauti domin sauraren zantawar su.

  • Malam Issoufou Boubakar Magaji kan kudurin Benin na hana jiragen man Nijar safara

    08/05/2024 Duration: 03min

    Jamhuriyar Benin ta sanar da cewa ta dakatar da fitar da man da Nijar ke yi har sai ta dube iyakar da ta rufe. Danna alamar saurare don jin cikakkiyar tatttaunawar tare da Bashir Ibrahim Idris.

  • Dr Abdulhakeem Garba Funtua kan yadda Isra'ila ke shirin yin gaban kanta wajen kai hari Rafah

    07/05/2024 Duration: 03min

    Kungiyar tarayyar Turai da Amurka sun gargadi Isra'ila a shirin da take yi na kai hari Rafah, duk da cewa alamu sun nuna cewa kasar bata da shirin dakatar da kudurin nata. Danna alamar saurare don jin cikakkiyar tattaunawar tare da Bashir Ibrahim Idris

  • Farfesa Dicko Abdurrahmae kan zaben Chadi

    06/05/2024 Duration: 03min

    Yau Litinin aka bude rumfunan zabe a kasar Chadi, don zaben shugaban kasa da zai kafa sabuwar gwamnatin Chadi da ta kasance karkashin mulkin soji na tsahon shekaru 3. Kan wannan batu Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Dicko Abdurrahmane daga jamhuriyar Nijar, wanda ya yi bayani kan yadda yake kallon zaben.

  • Farfesa Umar Pate: Kan Ranar 'Yancin 'Yan Jarida ta Duniya

    03/05/2024 Duration: 03min

    Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya, inda ake nazari a kan kalubalen da ma’aikatan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin inganta aikin. Sakamakon wannan biki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Umar Pate, shugaban Jami’ar Kashere, kuma shehun malami a bangaren horar da ‘yan jarida a Najeriya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.

  • Farfesa Kelani kan zargin da NNPCL ta yi wa wasu dillalan mai a Najeriya

    02/05/2024 Duration: 03min

    Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci.  Yanzu haka farashin litar man ya haura naira dubu biyu a wasu sassan Najeriyar, yayin da ake samun dogayen layuka a manyan birane irin su Lagos da Abuja da Kano.Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da farfesa Kelani Muhammed, kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron hirar da suka yi.

  • Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya

    01/05/2024 Duration: 03min

    Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu

  • Dr. Kasim Kurfi: Kan rashin tsayuwar karfin naira

    01/05/2024 Duration: 02min

    Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400. Sai dai a wannan makon Nairar ta sake samun tagomashi inda aka sayar dalar Amurka guda kan kasa da naira dubu 1,300.Ko me ya janyo rashin tsayuwar karfin Nairar, duk da irin matakan da bankin Najeriya ya ɗauka domin ba ta kariya? Tambayar kenan da muka yi Dr Ƙasim Kurfi, masanin tattalin arziƙi a Najeriyar.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da shi

page 1 from 2